Najeriya: Gwamna Zulum Ya Farfado Da Tsarin Samar Da Magungunan Dabbobi

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri

Sabuwar ma’aikatar gwamnatin jihar Borno ta dabbobi da kiwon kifaye da aka kirkiro don habbaka kula dasu ta gyara da maida ofishin kwamishinan da sakataren din-din-din dana mai bada shawara na zamani.

Haka nan Gwamna Zulum ya farfado da tsarin samar da magungunan dabbobi wanda baya aiki shekaru 7 da suka wuce sakamakon rashin samar da magungunan da kayan aiki.

Ma’aikatar ta samar da magungunan da sabon asusun banki daga bankin Keystone inda taci gaba dasa kudin cikin asusun don cigaba da ayyuka.

Kwamishinar ma’aikatar Comrade Juliana Bitrus w c eta bayyana hakan ranar litinin yayin bada jawabi ga manema labarai inda tace da hadin gwiwar sashin kula da ayyuka sun gyara sun gyara motoci uku da suka baci da kuma biyu da suka bawa jami’an sintiri.

Ta kara da cewa aikin kula da dabbobin yayi kyakkyawar alaka da ma’aikatanta da na kungiyoyi masu zaman kansu da ragowar ma’aikatau ciki harda ma’aikatar noma.

Haka nan tace ta kai ziyara sau da dama mayankar dake birnin Maiduguri ta Kasuwan Shanu don habbaka kiwon lafiya da kuma mahautan da kuma yadda za’a dinga kwashe musu shara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply