
By:Babagana Bukar Wakil, Maiduguri.
Kwamishinan lafiya na jihar Borno kuma sakataren kwamitin kar ta kwana ya yaki da cutar COVID-19 Dr Salihu Kwayabura ya bayyana cewa gwamnati ta fara biyan ma’aikatan kiwon lafiya wasu kudade na musamman.
Dr Kwayabura ya bayyana hakan a jama’a yayin da yake bada bayani kan cutar a Maiduguri.
Yace kwamitin na kula da mutane 145 da sukayi hulda da wadanda ke dauke da cutar.

Ya kara da cewa ana nan ana duba yadda za’a saukakawa mutane zaman gida don mutane su samu su dinga shan ruwa cikin sauki.
