Najeriya: Guguwa Ta Lalata Gidaje 600 A Jihar Kano

KANO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar bada agaji ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 6 da kuma lalata gidaje 600 da iska tayi a kananan hukumomi 4 dake jihar.
Dr Sale Jili babban sakataren hukumar ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a kano inda yace kimanin mutane 1, 752 ne suka rasa matsugunan su cikin sati daya.

Kananan hukumomin da abun ya shafa sune Gwale, Rimin Gado, Gwarzo da Kibiya. Jili ya bayyana cewa mutum daya ya makale a wayar wuta a unguwar Ja’in sai guda 5 da suka rasu a gini a karamar hukkumar Gwale.

Ya kara da cewa hukumar ta baza jami’an tsaron ta a yankunan da abun ya shafa don duba yadda abun ya faru da daukar kiyasin wadanda abun ya shafa.

San nan ya gargadi yankunan da suke da hatsarin ambaliyar dasu guji zuba shara a hanyoyin ruwa don kare kai daga ambaliyar ruwan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply