
Kungiyar masu kwalon kafa ta kasa wato NFF ta amince da yarjejeniya da Gernot Rohr da ya cigaba da zama kocin Super Eagles.
Amaju Pinnick, shugaban kungiyar na kasa ne ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a safiyar yau inda yace sun amince da Rohr.
Ya kara da cewa kungiyar NFF da Coach Gernot Rohr sun kammalla yarjejeniyar inda zai cigaba da zama kocin Super Eagles.

Haka nan yace a kullum NFF nada tabbas a kansh ida kokarin da yake yi inda yace a yanzu zasu iya samun nasarar shiga da kuma kara wasan duniya da kuma cin kofin. Kuma Rohr yasan da wan nan matakan da aka kafa masa.
Dandal Kura Radio ta tuno cewa Rohr ya karbi ragamar aikin daga hannun Sunday Oliseh a watan August na shekarar 2016.
