Najeriya: EFCC Zatayi Farautar Wadanda Suka Boye Kadarori A Kasar Ghana

magu large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC Ibrahim Magu yace yawancin wadan da suka kwashe kudin kasa sun boye ne a kasar Ghana.

Yayin da yake Magana a Abuja ranar Juma’a Magu yace hukumar na nan na shirye shiryen zuwa kasar su binciko kudaden. Shugaban na EFCC ya bayyaana hakan bayan da tawagar Chartered Institute of Public Resources Management and Politics suka kai masa ziyara a hedikwatar hukumar dake Abuja.

Acewar hukumar ta EFCC ta hada gwiwa da takwararta ta kasar Ghana kan binciko abubuwan day an Najeriyar suka boye. Haka nan yace suna nan suna shirin zuwa kasar ta Ghana don dawo da kadarorin gida.

San nan ya roki yan Najeriya dasu yi amanna da hukumar hade da basu bayanai kan ayyukan cin hanci da ake gudanarwa a kasar. Magu yayi kira gabyan Najeriya da suyi watsi da rahotannin karya da ake yadawa a wasu kafafen watsa labarai a kanshi inda ace ayyukan hukumar a bayyane suke.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply