Najeriya: Dattijan Arewa Maso Gabas Sunyi Kira Da A Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Arewacin Borno

Photo by Babagana

Photo by Babagana

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wasu dattijan yankin Arewa maso gabas karkashin kungiyar Patriotic Elders Council sun bukaci da a tashi tsaye kan hare-haren yan kungiyar Boko Haram a arewacin Borno.

Kungiyar tayi kiran ranar litinin inda ta bukaci shugabannin yankin das u jagoranci kiran yan kungiyar ta Boko Haram dasu mika kansu.

Kiran yazo bayan awanni 24 bayan da rundunar tsaron kasar ta bayyana cewa 13 daga cikin yan kungiyar ta Boko Haram sun mika kansu tare da mata 6 da kuma yara 17 daga kauyen Kodila village.

Kungiyar tace bata ji dadin yadda yan kungiyar ta Boko Haram suka yiwa tawagar gwamnan jihar Borno kwantan bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Baga don karbar yan gudun hijira.

Haka nan kungiyar ta fitar da takardar ta hannun babban sakataren ta Simon Shango wanda yace kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta na yadda wasu shugabannin yankin da masu ruwa da tsaki suna gidajensu a Abuja da sauransu amma suna kushe jami’an soji adan aka kai wadan nan hare-hare.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply