Najeriya: Da Yardar Gwamnati Nayiwa Wasu Hukumomin Gwamnati Gwanjon Motoci – Magu

magu large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC Ibrahim Magu yace wasu daga cikin kayan da aka kwato anyiwa ma’aikatun gwamnati gwanjonsu.

Babban lauyan gwamnati na kasa wato Abubakar Malami ya zargi Magu da kin bayyana abubuwan da aka kwato din daga wadanda suka kwashe.

Malami ya zargi Magu da said a wasu daga cikin kayan da aka kwato ga mutanensa inda ya bukaci kwamitin binciken karkashin mai shari’a Ayo Salami daya sa Magu ya bayyana yadda ya saida su.

Magu ya bayyana cewa da yardar gwamnati yayi gwanjon motoci ga hukumar haraji ta kasa da ma’aikatar kula da iftila’I, hukumar karbar haraji ta hanyar gwanjonsu.

Haka nan Magu yace akwai kimanin motoci 450 da aka kwato da har yanzu ba’a siyar ba duk da gwamnatin ta amince da hakan.

San nan yace wasu daga cikin hukumomin basu biya ba amma an yanke abinda za’a dinga a kudin shiga nan ma’aikatar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply