Najeriya: Boko Haram Sun Kai Hari Karamar Hukumar Monguno

bh small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mazauna day an kungiyar sa kai dake karamar hukumar Monguno a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya sun ce da badan daukin da jami’an soji suka kai musu da jirage masu saukar ungulu bad a harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai musu zai fi na kauyen Faduma dake karamar hukumar Gubio.

Acewar mazauna yankin, maharan sun kona gurin yan kungiya mai zaman kanta ta majalisar dinkin duniya kurmus da kuma wasu guraren nay an kungiyoyi masu zaman kansu.

Haka nan sunce maharan sun rarraba wasiku ga mazauna yankin inda suke ce musu kar suyi aiki da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma aikin gwamnati.

San nan sunce mutane da dama sun samu raunuka yayin da sukayi luguden wuta wanda ya mamaye asibitin yankin na Monguno.

Shugaban rundunar sojin, Lt Gen Tukur Yusufu Buratai ya taya jami’an murna da wadanda ke sansanin Super Camp dake Monguno wajen jajircewarsu da nuna jarumta yayin harin na Monguno.

A rahoton da Col. Sagir Musa, daraktan rundunar na hulda da jama’a na rundunar ya fitar yace shugaban rundunar ya yabawa rundunar yanda suka dauki mataki kan yan ta’addan da yadda suka kamasu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply