Najeriya: Bayan Cutar Corona Akwai Wasu Cututtuka Da Suka Addabi Yan Gudun Hijira a Jihar Borno – MSF

idps
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Babagana Bukar Wakil, Maiduguri

Shugaban kungiya mai zaman kanta ta Medecins Sans Frontieres wadda aka fi sani da Doctors Without Borders Siham Hajaj yace cutar Coronavirus na yiwa yan gudun hijira miliyan 1.5 da masu bada taimako barazana a jihar Borno.

Ya bayyana haka ne sakamakkon iftila’in da ake ciki na cutar da kuma cutar malaria, rashin abinci mai gina jiki da kuma wasu cututtukan da ake dauka cikin ruwa.

Hajaj ya bayyana hakan a rahoton daya fitar a Maiduguri inda yace COVID-19 ba ita kadai ce take damun mutane a jihar ba.

Haka nan yace yan gudun hijira dake sansanoni da wasu matsugunan sun ga abubuwa da daman a tashin hankali kamar yaki, cututtuka da rashin abinci mai gina jiki.

Hajaj y ace dole aci gaba da bada taimako gay an gudun hijira saboda za a iya samun bullar wasu cututtukan kamar rashin abinci mai gina jiki, malaria, kyanda, da kwalara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply