Najeriya: Bankin Micro Finance Na Jihar Borno Ya Raba Bashi Ga Kananan Yan Kasuwa

bank
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Bukar Ali Mishemi, Maiduguri.

An kafa bankin Borno State Micro Finance a shekarar 2015 don a ragewa jama’a radadin ta’addancin Boko Haram a jihar. An gano hakan bayan da wakilin Dandal Kura Radio Bukar Ali Mishemi ya zanta da babban Manajan bankin Dr Belli Alhaji Ibrahim.

Babban Manajan ya bayyana cewa a yanzu bankin na raba bashi ga masu kananan san’oi dake kasuwar litinin a Maiduguri. A kudaden da bankin masana’antu wato Bank of Industry da gwamnatin jihar Borno suka bayar.

A wani bangaren Dr Belli yace a bashin da suka bayar kwanaki ba a samu cigaba ba don da yawa basu biya kudaden da aka basu ba. Haka nan yace a wan nan karon kungiyoyi ne zasu tsayawa masu karbar bashin saboda su sunsan wadanda ke tare dasu.

San nan yayi kira ga wadanda suka mafana dasu godewa gwamna Babagana Umara Zulum kan yadda ya shafe musu kashi 50 na kudaden kuma ya bukace su dasu yi amfani Dasu yadda ya kamata don wasu su amfana nan gaba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply