Najeriya: Anyi Garkuwa da Mutane A Cocin Afrika Ta Kudu

south Africa
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yansandan kasar Afrika ta kudu sunce mutane biyar ne suka rasu kuma aka kama mutane arba’in bayan da akayi garkuwa da mutane a wata coci dake kusa da Johannesburg.

Rahoton yace yansandan da jami’an sojin wadanda suka bada rahoton harbe-harben da akayi a cocin International Pentecostal Holiness Church dake garin Zuurbekom sunce sun samu gawar mutane 4 da aka kashe kuma aka kona a cikin mota sai kuma wani jami’in tsaro da aka harba a cikin mota.

Haka nan yansandan sunce sun ceto wasu maza, mata da yara wadanda aka tsare a cikin cocin.

San nan sun kara da cewa fiye da bindigogi 30 aka samu kuma ana kyautata zaton rigimar tsakanin yan cocin ne.
Kwamishinan yansandan yankin yace badon shiga tsakanin da yansanda sukayi ba da an yi mummunan lamari.

Haka nan yace cikin wadanda aka kama akwai yansanda, da jami’an tsaro.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply