Najeriya: An Rabawa Matuka Mashinan Keke NAPEP Lambobi Da Kaloli A Jihar Borno

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamishinan ma’aikatar sufuri na jihar Borno Hon Dr Abubakar Tijjani ya kaddamar da rabon takardar shaidar tuki da lambobin mashin din Keke Napep hade da kalar da za’a gane na kowace unguwa a cikin birnin- Maiduguri.

An gudanar da bikin a ofishin gyaran moyovin Borno Express dake kan titin Baga a Maiduguri.
Yayin da yake yiwa shugabannin Keke Napep din jawabi kwamishinan ya bayyana musu cewa za’a dauki bayanan masu masu mashinan da matukan su wanda hakan ba yana nufin dakatar da sana’arsu ba ko bin diddiginsu illa gyara musu da tsaftace musu sana’arsu.

Haka nan yace mutanen jihar ne a gaban Gwamna Babagana Umara Zulum inda yayi kira garesu da su bawa gwamnatin hadin kai, haka nan yayi kira garesu dasu adana takardun shaidar da aka basu don duk wanda ya batar sai ya biya za’a sake bashi.

Daraktan ma’aikatar Engr. Babagana Moruma ya bayyana cewa saka karfe jikin mashinan zai kawo raguwar hadarurruka.

Wasu daga cikin yan kungiyar matukan sun yaba da wan nan aikin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply