Najeriya: An Mika Magu Zuwa Sashin Binciken Manyan Laifuka

magu large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na rikon kwarya wato Ibrahim Magu ya bayyana gaban kwamitin dake gudanar da bincike a kansa bayan da babban lauyan kasa kuma kwamishina shari’a na jiha Abubakar Malami ya bada korafi a kansa.

Mai shari’a Isa Ayo Salami tsohon shugaban kotun daukaka kara ne yake jagoranta, rahotanni na nunu da cewa an tsare Magu a daren jiya bayan ya gama amsa tambayoyi daga kwamitin binciken.

Haka nan anyi awon gaba da magu daga fadar shugabn kasar zuwa sashin binciken manyan laifuka ta Force Criminal Investigation Department da misalin karfe 10.15 na dare.

An kai ruwa rana tsakanin yansandan dake rakiyarsa da jami’an tsaron na farin kaya kafin a kaishi inda aka ajiye shin.

Inda akace an sa shi a wata farar motar Hilux wadda aka rubuta 371 D kuma aka bukaci ya zauna a bayan motar, amma bayan musayar yawu aka barshi yah au motarshi ta aiki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply