
Rundunar tsaron najeriya tace jami’an tsaron kasar a shirye suke kuma sunyi shirin ko ta kwana bayan da kasar amurka ta bayyana musu cewa yan kungiyar Al-Qaeda da ISIS na shirin shiga kasar.
Mai kula da harkar yada labarai na rundunar The Major General John Enenche ne ya bayyana hakan yayin bada jawabi kan ayyukan rundunar a kasar a Abuja.
Yace Amurka tace Al-Qaeda da ISIS na neman hanyar da zasu shiga kudancin kudancin kasar sai kuma su shiga arewa maso yammacin kasar.

Dagvin Anderson kwammanda rundunar kasar amurka a Afrika ya bayyana cewa a satin day a gabata.
Enenche ya jaddada cewa jami’an a shirye suke akan wan nan kalubalen.
Haka nan Enenche ya musanta zargin da akewa jami’an sojin dake garin Baga na jihar Borno kan yin wasu ayyuka bawai yakin da aka tura suba inda yace wan nan zargi ne mara tushe
