Najeriya: Rundunar Operation lafiya Dole Ta Kubutar da Mutane 33

Nigerian_Nigeria_army_soldiers_military_combat_field_uniforms_007
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar operational lafiya dole mai yaki da kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta sami nasarar kubutar da wasu fararen hula guda 33 a yayin wani aikin sintiri da suka gudanar a kananan hukumomin Damboa da kuma Bama dake jahar Borno.

Rundunar ta kai wani farmakin hadin gwiwa, har ila yau ta sami nasarar kwato makaman Ak 47 guda 6 a hannun mayakan.

Wannan jawabin ya fitone a wani sako da diraktan hulda da jama’a na rundanar, brig. Janar texas chukwu ya rattabawa hannu.

Sakon ya cigaba da cewa, sojojin sun kuma sami nasarar harbe wani dan kungiyar boko haram har lahira a kauyen Darel salam dake karamar hukumar Bama.

Chukwu ya kara da cewa, an mika mutanen hannun hukuma domin sada su da iyalen su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply