Najeria: Za’a Maida AyyukanAikin hajji Ta Hanyar Na’ura Mai Kwakwalwa

nahcon small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar aikin Hajji ta kasa wato NAHCON da hadin gwiwar hukumar ilimin fasaha ta kasa wato NITDA sun kammalla shirye shiryen maida ayyukan aikin Hajjin ta hanyar na’ura mai kwakwalwa a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan ganawar da suka yi ranar Talata 9 ga watan Juni na shekarar nan a dakin taro na hukumar aikin hajji ta kasa.

Yayin da yake jawabi kwamishina shugaban hukumar aikin Hajjin Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana amfanin na’ura mai kwakwalwa a wan nan karnin na 21, inda yace hakan zai zai karfafa ayyukan hukumar ta hanyoyin da suka dace kuma za’a samu cigaba.

A nashi bangaren shugaban tawagar NITDA ya bayyana hanyoyin da zasu bi na tsara ayyukan da suka dace inda suka ce dole ma’aikatan su shirya tsaf don gudanar da aikin yadda ya dace. Inda yace yakamata su dauki aniyar komawa kan tsarin.

Haka nan yace da wan nan sabon tsarin za’a habbaka jin dadin alhazan kuma sunce hakan zai habbaka harajin hukumar aikin Hajjin ta hanyar yanke wasu kudaden da ake kashewa ba bisa ka’ida ba.

A wani bangaren shugaban hukumar aikin Hajjin da tawagarsa sun ziyarci majalisa bayan da kwamitin yan majalisar tarayyar suka gayyace su kan suji shirye-shiryensu na shekarar 2020 don suji inda suke neman taimako.

Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa ya yaba da tawagar inda ya tabbatar musu cewa a shirye suke idan suna neman taimako. Haka nan Abubakar Hassan Nalaraba ya yabawa hukumar aikin hajjin inda yayi alkawarin bada nasu taimakon.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply