Nadin Sabbin Hafsoshin Tsaro Da Akayi A Ranar Talata Ya Kasance Babban Cigaba Ga Jama’ar Jihar Borno.

FB_IMG_1611771508404
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri
Nadin sabbin hafsoshin tsaro da akayi a ranar Talata ya kasance babban cigaba ga jama’ar jihar Borno.

Hakan yazo da mamaki ga jama’a duk da irin korafe korafen da ake yiwa shugaba Buhari nay a canza su domin gazawar su a yaki da yan kungiyar Boko Haram.

Sanarwar da mai bada shawara na musamman kan yada labarai ga shugaba Buhari Femi Adesina ya fitar yace bayan nadin sabbin hafsoshin, tuni tsohon hafsan rundunar sojoji yayi ritaya.

Wani mazaunin garin Maiduguri Mal Haruna Shema Gomari yace sun ga abin da Janar Buratai yayi haka kuma sun san abin da janar I Attahiru da janar Lucky Irabor sukayi.

Yace dukkan su sunyi aiki da shirin operation Lafiya Dole kuma suna addu’an Allah ya basu damar wanzar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Borno da yankin arewa maso gabas dama kasa baki daya.

Haka nan wani mai suna Alh. Gambo Hausari yace janar Buratai yayi aiki matuka kuma yayi kokari, yana addu’ar Allah yasa wadanda aka nada a yanzu su yi aiki na kwarai wajen yakar yan kungiyar Boko Haram.

Wani matukin mota mai suna Musa Adam yace sun ji dadin samun wannan labari kuma sunyi farin ciki da hakan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply