Mutanen Zabarmari Sunce Tsaro Suke Bukata Ba Abinci Ba

farmers-at-work-agriculture
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A kokarin kiran da ake yiwa gwamnatin tarayya ta samar da tsaro akan yan kungiyar Boko Haram bayan da suka kai hari garin Zabarmari dake jihar Borno inda yan kungiyar suka kasha manoma fiye da 60 mutanen yankin sun roki gwamnatin tarray cewa sunfi bukatar a samar musu tsaro kan basu abinci.

Wailinmu ya rawaito mana cewa gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar bada agaji ta aika motocin abbinci yankin da kayan amfani don ragewa mutanen yankin radadin harin da suka fuskanta.

Amma mutanen yankin sunce sunfi bukatar a samar musu tsaro maimakon kayayyakin da ake kai musu.

Wani mazauna yankin mai suna Usman Mohammed dan shekaru 58 yace a ranar bai samu yaje gona ba shida yaransa 2 saboda zaben kananan hukumomi inda da shima tuni an kasha shi.

Haka nan yace wasu daga cikin wadanda abun ya shafa matasa ne wadanda suke zuwa aiki su samu na kashewa.

Wani day a tsira da ransa mai suna Mohammed Hassan ya bayyana cewa wadanda suka kai harin basu da yawa basufi 7 ba.

Haka nan wani mai suna Musa Zabarmari dan shekaru 45 yace maharani sun samu damar zaben kananan hukumomi da ake inda suka kai harin don hankalin jami’an tsaron na kan zaben.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply