Mutane guda 10 da akayi garkuwa dasu a masallacin Jibia a jihar Katsina

Mutane guda 10 da akayi garkuwa dasu a masallacin Jibia a jihar Katsina sun tsere daga hannun wadanda sukayi garkuwa dasu jiya juma’a a Zurumi na Jihar Zamfara

Idan za iya tunawa a ranar litinin da misalign 12:30 ne masu garkuwa da mutane suka kwashe masu ibadu 40 yayin da suke salla a masallacin dake Jibiyan jihar Katsina inda daga bisani rundunar soji da yan sanda suka ceto 30 daga sansanin yan bindigar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandar jihar Gambo Isa, shi ya sanar da hakan inda yace sun tsere ne daga miyagun jama’a.

Wani mazaunin jibiya daya nei a sakaye sa yace maza guda 7 da mata 3 se jariri daya ne suka samu tserewar inda iyalan daya daga ciki ya bayyana cewa babu wani kudin fansa da suka bayar.

Mai shayar wa daga cikin wadanda suka tseren ta bayyana cewa wata mace dake auren daya daga cikin yan bindigan ne ta taimaka musu suka tsere inda ta umurce su da su gudu bayan ta kunce dauri da aka musu.