
Rikici tsakanin sojojin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kungiyoyin mayaka a cikin watan Disamba ya haifar da raba mutane 5,000 da muhallinsu.
A cewar wani rahoto na Ofishin Kula da Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya, (UNOCHA), ‘yan gudun hijirar sun koma kauyukan Buginanyana, Kaina da Luhando da sauransu zuwa yankin kiwon lafiya na Kibua a yankin Walikale.
A cewar UNOCHA, an wawushe gidaje 85 sannan wasu mutane dauke da makamai sun lalata mata da dama.

Lamarin ya tunzura mutane barin muhallan su a Nyabiondo wadanda suka gudu zuwa cikin daji suka cigaba da zama a cikin dazuka har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoton.
Tun daga lokacin rikicin ya fadada zuwa Myandja, arewa maso yammacin Masisi kan babbar hanyar Loashi-Lushebere wanda hakan ya tilasta fararen hula a yankin barin gidajensu suka gudu zuwa dazuzzuka, a cewar UNOCHA.
