Mutane 23 Suka Rasa Rayukansu A Sanadiyan Hatsarin Baban Mota A Jihar Niger

Niger State
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Akalla mutane 23 ne aka tabbatar sun rasa rayukan su 33 kuma sun jikkata yayin da hatsarin babban mota ya abku a kauyen Masha dake hanyar Makera zuwa Mokwa na jihar Niger.

An ruwaito cewa babbar mota zata nufi kudancin kasar ne cike da shanaye, da amfanin gona dama mutane da suka kai 55
Sai dai a lokacin da abin ya faru an nemi direban motar da Karen motar sa

ba’a same sub a inda shaidun gani da ido suka tabbatar da cewa tserewa sukayi
A halin da ake ciki an kai wadanda suka saun rauni babban asibitin Mokwa domin karban kulawa sannan aka aje wadanda suka rasu a dakin aje gawarwaki

Komandan shiyyar na hukumar hana hadura Mr. Joel Dagwa, ya tabbatar da hakan cikin sanarwa me kunshe da cewa hatsarin ta abku kadai da babbar motar na DAF wanda yace gudu da sukeyi ne ya wuce misali har yayi sanadiyyar hatsarin
Ya kuma ce motar ta tashi ne daga jihar Kebbi ta nufi jihar Lagos, ya kuma kara da cewa dukkan pasinjojin dake ciki mazane.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply