
Mai Magana da yawun rundnnar yan sandan jihar Bauchi DSP Ahmed Muhammad Wakil yace an tabbatar da mutuwar wasu mutane 20 sannan 2 sun samu mummunar rauni sakamakon hatsarin mota a kan titin Bauchi zuwa Maiduguri.
DSP Wakil ya bayyanawa wakilinmu a jihar Bauchi cewa hatsarin ya auku ne a wajen garin na Bauchi.
Ya kara dacewa tuni a ka kai gawakin zuwa dakin ajiye gawa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa sannan mata biyu da suka rayu daga hatsarin suna samun kulawa a asibitin.

Wani wanda abin ya faru akan idon sa Musa Shehu Buji ya bayyanawa wakilinmu cewa hatsarin ya auku ne tsakanin motoci 2 da suka hadu a Mangorori a yankin Tirwaun dake da nisan kilomita 3 daga babban birnin jihar na Bauchi.
Yace mota kirar hummer bus mallakin Borno Express da ya nufe Maiduguri daga Jos dauke da fasinjoji 18 sai kuma kirar VW golf da ya taso daga Misau zuwa Bauchi dauke da fasinjoji 4 a ciki.
