Mutane 16 Suka Rasa Rayukan Su Ciki Harda Yara Kananan Guda 9

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mutane 16 ne suka rasa rayukan su ciki harda yara kananan guda 9, yayin da yan ta’addan Boko Haram suka kawo farmaki birnin Maiduguri na yankin arewa maso gabas.

Yan ta’addan sun mamaye wani bangaren na garin dauke da manyan bindigogi da wasu yan kunar bakin wake.

Adadin wadanda aka rasan ya haura 16 kamar yadda wani dan tsaron sa kai Baba kura Kolo ya shaidawa manema labarai, da kuma yara kanana maza guda 9 da suka rasa rayukan su yayin da abin fashewa ya sauka akan su a filin wasan kwallo.

Haka kuma wani dan tsaron, Umar Ari ya tabbatar da adadin, kuma yace zai iya haurawa fiye da hakan ganin cewa da dama sun jikkata.

Shi kuwa shaidar gani da ido, Sama’ila Ibrahim yace mayakan sun tsalleke iyaka da aka tona suka shigo birnin ta kauyen Boboshe da suke da karfin a wurin, yayin da jama’a kowa ya watse domin neman tsira.

Rundunar sojojin Najeriya sun dakile harin yayin canjin wuta da sukayi da yan ta’addan.

Tun shekarar 2009 da aka fara ta’addancin, tashin hankalin ya halaka mutane dubu 36 kuma ya watsar da akalla miliyan dubu 2 daga gidaje da yankunan su.

Rikicin ya watsu kashen dake makwabtaka da Najeriya na jamhuriyyar Nijar, Kamaru da Chadi wanda ya haifar da rundunar hadin kai domin yakar yan ta’addan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply