Miyetti Allah ta bayyana abubuwan da za’ayi na kawo karshen rikicin makiyaya da manoma

miyetti Allah
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya tace zata yadda duk wata doka da gwamnati zata saka a yankin kudu maso gabas idan gwamnati ta roki su dena fadan tsakanin yankunan da makiyaya.

Shugaban kungiyar na yankin kudu maso gabas Alhaji Gidado Sidikki ne ya bayyana hakan yayin da yake Magana da manema labarai a garin Awka dake jihar Anambra .

Yace kungiyar dake yankin kudu maso gabas na tare da duk wata doka da gwamnatin zata kafa na kawo karshen rikicin tsakanin Fulani makiyaya da manoma idan har hakan zai amfani dukkaninsu.

Acewar Siddiki abinda gwammnan yayi dai dai amma tabbatuwar dokar ya kamata ayi abun da zai kawo zaman lafiya da dai-daito.

Haka nanyace suna horar da Fulani makiyaya kan hanyoyin kiwo a jihohi 36 dake fadin kasar hard a Abuja da kuma gudanar da taruka tsakanin gwamnati, manoma da makiyaya a yankunan da abun ya shafa.

San nan yace ya yarda da cewa hakan zai kawo karshen rikicin day a dade yana addabar manoma da makiyaya a kasar.

Haka nan kungiyar tace yawancin mambobinta basu da masaniyar hanyoyin kiwon don haka yake kiran gwamnati data cigaba da horar da makiyayan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply