
Ministar kula bada agaji da iftila’i Sadiya Farouq tace gwamnatin tarayya bata da niyyar sake daukar ma’aikatan N-Power cikin hukumar ma’aikata ta kasa.
Ministar ta bayyana hakan tabakin mataimakiyar Daraktan ma’akatar Rhoda Ilayyada labaran karya na daukar ma’aikatan N-Power .
Haka nan tace anja hankalin ma’aikatar kan labbaran karyar da ake yadawa a kafafaen sada zumunta cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da bayani gay an Najeriya kan cewa zai dauki ma’atan N-POWER na farko a hukumar ma’aikata ta kasa.

Inda tayi kira ga jama’a dasu yi watsi da sakon su dauke shi a matsayin labarin karya.
Haka nan tace duk wani sako daga The N-Power ko National Social Investment Programme za’a tura shi inda ya dace.
