Ministar Agajin Da Walwalar Jama’a Ta Jajantawa Yan Sansanin Gudun Hijiran Da Gobarar Ya Shafa.

sadiya
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministar agajin gaggawa da walwalar jama’a, Sadiya Farouq, ta jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukan su a gobarar wutar daya afku a sansanin yan gudun hijira dake jihar borno.

Shugaban agajin gaggawa na jihar borno, Yabawa Kolo, yace, gobarar wutar ta bar mutane 7,200 ba muhalli ,yayin da sama da dakuna 1200 suka kone sakamakon gobarar.

A wata sanarwa, ranar alhamis da babban sakataren Bashir Alkali ya bayyana, inda mataimakiyar daraktan yada labarai, Rhoda Iliya ta rattabawa hannu, an bayyana gobarar a matsayin abu maras so.

Ministar ta bada umarnin raba kayan tallafi a sansanin nay an gugun hijiran ga wadanda gobarar ta shafa.

Sadiya Farouq ta yabawa Kolo da tawagar sa kan ziyartar sansanin da kuma jajantawa wadanda suka shafu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply