Ministan Tsaro Yace Zaa Dawo Da Daliban Da Aka Sace A Jihar Katsina Cikin Awanni Kadan.

Defence headquaters
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan tsaro Major General Bashir Magashi ya tabbatar da cewa dukkanin daliban makarantar nan da aka sace a jihar Katsina zasu dawo gida nan nan day an awanni.

Ya bayyana hakan a jiya yayin day a jagoranci tawagar gwamnatin tarayya ciki hard a shugabannin tsaro zuwa jihar ta Katsina don jajantawa iyayen yaran da aka sace din da kuma gwamnatin jihar.

Minister yakai ziyara bayan sace daliban fiye da 300 da yan bindiga sukayi.

General Magashi yace wan nan kalubalen da ake samu ya kamata jamian soji da yansanda da sauran hukumomin tsaro su tashi tsaye su tabbatar cewa an ceto yaran.

San nan ya jaddada cewa bai kamata ana kyale yan bindigar suna yin abinda suka ga dama ba, kuma ya kamata a bayyana su a matsayin yan taadda saboda ayyukansu a yankin arewa maso kudancin kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply