
Ministan Tsaro Manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ake fama dashi abune mai wuyan sha’ani duba ga yanayin matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a cikin kasar.
Magashi yana wannan bayanin na a wajen bikin yaye sojoji dari da takwas a kwallejin sojojin ruwa dake onne a jihar Rivers.
Ya kuma kara da cewa sojojin na aiki ne a yanayi mara dadi.

Ministan wanda shugaban sojin kasa General Gabriel Olonisakin ya wakilta yace kasar najeriya da kuma gabar tekun gini sun jima suna fuskantar matsalar rashin tsaro a bangarori daban daban.
Magashi ya kuma kara da cewa annobar cutar COVID-19 ta sake kawo kuma baya a bangaren tsaron.
