Ministan Sadarwa Yace Rajistan Lambar Shaidar Zama Dan Kasa Zai Bunkasa Tattalin Arziki .

images (26)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya tace samun lambar shaidan rajistan zama dan kasa abu ne da zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa cikin dan kankanin lokaci.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Dr. Isa Pantami shine ya bayyana haka a wani zantawa da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Dr Pantami yace wannan tsarin samar da shaidan dan kasa ba a baiwa dan Najeriya lambar shaidan dan zama kasa bane, ya zama wajibi kowa a Najeriya ya mallaki katin shaidar zama dan kasa cikin kankanin lokaci

Daga karshe ministan ya shawarci yan Najeriya da su samar da katin su a cikin lokacin da ya kamata domin kiyaye fuskantar wahalhalu a cikin rayuwar yau da kullum.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply