
Kungiyar wasanni ta kasa karkashin shugabanta ministan matasa da wasanni Mr Sunday Dare a tarown da suka gudanar ranar 15 ga watan December 2020, uinda suka amince da karbar bakuncin wasannin na NSF 2020 daga 14- 28th ga watan Fabarairu 2021.
Ministan ya bayyana cewa akwai bukatar daukar matakan da suka dace kan annobar COVID19 kuma akwai yarjejeniya da ma’aikatar lafiya dama kwamitin yaki da cutar ta Corona.
Idan za’a iya tunawa wasannin na kasa da akayiwa lakabi da ‘EDO 2020’ an maida shi gaba wanda a da za’a gudanar a watan Marriis na farkon shekarar nan amma saboda annobar ta COVID-19 aka dage saboda yaduwar cutar.

