Ministan Lafiya Osagie Ehanire Yace Zai Kokarin Ganin Likitoci Sun Dena Zuwa Aiki Kasashen Waje

min of health Elanare small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan lafiya na kasa Dr Osagie Ehanire yace gwamnatin tarayya zatayi yadda ya dace don ganin an karfafawa ma’aikatan kiwon lafiya gwiwa akasar.

Ehanire ya bayyana hakan yayin da yaje duba aikin asibitin cutar daji dake Abuja.

Yace yaji kalubalen da likitoci suke fuskanta da yadda suke barin kasar don haka suna nan suna shirin yadda zasu gyara kudadensu a asibitocin a kasar ta yadda bazasu dinga sha’awar barin kasar ba.

Haka nan yace asibitin yayi matukar kokarin yayin cutar annobar COVID-19 inda yace zai kokari yaga gwamnati ta tabbatar da likitocin sun zauna a kasar.

Babban daraktan asibitin Dr Jaf Momoh asibitin yayi kokarin ganin ya karfafawa likitocin gwiwar aiki a kasar.

Haka nan kan sabon asibitin cutar daji da ake ginawa ministan yabawa shugabannin asibitin shawarar amfani da kayan aikin yadda ya dace inda yace bayan an gama zai sama musu kudin shiga.

San nan ya yabawa ma’aikatan asibiin kan ayyukan da sukeyi kuma ya basu shawar das u shirya don akwai yiwuwar sak eballewar cutar COVID-19 don yanzu wasu kasashen sun fara fuskanta.

Haka nan yace yanzu an bude makarantu kuma mutane na shiga da fita kasashen waje don haka yamakata a shirya ayyukan gaggawa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply