Mazauna Karamar Hukumar Dikwa Sun Bayyana Jin Dadinsu Bayan Sojoji Sun Samu Galaba Kan Yan Kungiyar Boko Haram

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mazauna day an gudun hijira dake garin dikwa sun bayyana jin dadinsu yadda sojojin Najeriya suka fatattaki yan kungiyar Boko Haram suka samar da zaman lafiya a garin.

Jami’an sojin sun dawo da zaman lafiya a garin na Dikwa bayan da suka dauki aniyar kawo hargitsi a garin yayin da suka kai hari wani yanki na garin ranar Juma’a.

Idan za’a iya tunawa ranar juma’ar yan ta’addan sun kai hari karamar hukumar ta Dikwa amma sojojin yankin na Operation Lafiya Dole sun dakile harin bayan da suka fafata na awanni da dama.

Kwamanda mai kula da yankin Maj Gen Abdul Khalifa ya ziyarci garin don ganewa idonsa yadda abun ya faru da kuma samun rahotanni daga bakin mazauna garin.

Haka nan yace a yanzu komai ya koma dai-dai kuma mutane na komawa gidajensu.
Acewarsa jami’an sojin sun samu nasara kuma sun zagaye yankin baki daya kuma har yanzu suna kan binciken gano yadda abun ya faru.

Haka nan wakilinmu Ali Muhammed Zanna gya hada mana rahoton cewa a yanzu garin an samu lafawar lamarin kuma mutanen da suka gudu yayin da jami’an na soji day an kungiyar Boko Haram ke fafatawa sun koma gida

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply