Mazauna jihar Bauchi sunyi zanga zanga sakamakon kusawar yan bindiga wani yanki inda suka sace wata mata mai shayarwa.

Hukumar kula da yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya tace ya kamata duniya ta kula da abubuwan dake faruwa a yankin Shara musamman yankin tabkin chadi.

Da yake jawabi a wani taro a Abuja bayan ziyarar da ya kai yankin arewa maso gabas da wasu bangare na kasar Kamaru don yin shirye shirye na farfado da yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram dana ISWAP a yankin, mataimakin babban jakadan ayyuka na hukumar Raouf Mazou yace ana bukatar kasa da kasa fiye da baya akan abubuwan da yake faruwa a yankin tabkin chadi.

Yayin ziyarar ya gana da jami’an gwamnati da yan gudun hijira a yankin tabkin chadi domin jin ta bakin su akan yanayin da suke ciki da kuma duba ta yadda za’a taimaka musu wajen sake gina rayuwar su.

Mazou ya iso Najeriya a ranar Litinin da ta gabata, yace ya ziyarci Kamaru inda yace akwai sama da yan hijira dubu dari 1, kuma ya ziyarci sansanoni wanda ya hada da Banki inda akwai sama da yan hijira dubu 40 da suka dawo daga Kamaru.

Ya bayyana cewa a jihar Borno cewa ya gana da hukumomi da yan hijira da yan gudun hijira da suke cikin tashin hankali.

Yace akwai yan Najeriya kusan dubu dari 1 da 70 a Nijar sannan kusan dubu 16 a kasar Chadi.

Haka kuma yace mai da yan gudun jihar yana da nasaba da jihar Borno kasancewar sa cibiyar rikicin Boko Haram.

Ya bayyana cewa a yanzu hukumar tana kokarin hada guiwa da gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Borno.