
Mazauna garin Maiduguri sunyi kira ga gwamnatin jihar Borno domin ske bude hanyar Maiduguri zuwa Damboa domin samun damar kai kayaki zuwa kasuwanni a kudancin jihar Borno.
Hajiya Fati Abubakar ita tayi kira a cikin shirin gidan radio Dandal Kura na koken masu sauraro inda tace yan kasuwa suna wahala wajen kai kayaki daga Maiduguri zuwa sauran wurare a kudancin jihar Borno.
Tace kasuwanci ta hanyar Maiduguri zuwa Damboa yafi sauki, amma a yanzu rufe hanyar da akayi yana sanya yin kwanaki a hanya kafin a isa inda ake so.
Ta kara dacewa suna asarar kayakin su kafin su isa inda suke a bukata, dan haka tayi kira ga gwamnatin jihar Borno da ta bude hanyar domin inganta kasuwancin su.
