Matatan Mai Dangote Zata Sayar Da Danyen Mai Ga Gwamnatin Tarayya .

DANGOTEWIDE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele yace ana shirye shiryen fara tace mai a matatan mai na Dangote kuma zata fara saidawa a naira idan ta fara aiki.

Yace za a fara kawo takin shuki na Dangote a watan Maris domin taimakawa wajen bunkasa harkar noma a kasar nan.
Emefiele ya bayyana haka yayin ziyarar duba ayyuka a matatan Dangote a Ibeju Lekki a jihar Legas.

Yace ayyukan dala biliyan 15 da kamfanin Dangote ya shirya zai hana kasar Najeriya kashe kashi 41 wajen shigo da man fetur.

Yace bisa yarjejeniyar da akayi da kamfanin man fetur ta kasa, matatan main a Dangote zata siya danyen mai a naira kuma zata samar da ita ga yan Najeriya.

Yace za a gama matatan a kashin farko na shekarar 2022 kuma yace zai kawo karshen matsalar tallafin man fetur a kasa.

Yace babban bankin Najeriya ta bada biliyan dari 1 domin aiwatar da aikin, yace sauran bankunan ma a shirye suke wajen taimakawa kasuwancin Najeriya domin inganta tattalin arziki.

A nashi bangaren Alh. Aliko Dangote yace takin shuki zai iya samar da dala biliyan 2 da digo 5 sai kuma matatan zai ishi Najeriya da wasu kasashe a fadin duniya.

Daga karshe yace aikin zai samar da ayyuka ga yan Najeriya a bangarori da dama.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply