Mata Da Dama Suna Fama Da Damuwa Wanda Yake Kai Ga Matsalar Kwakwalwa.

damasakwoman
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Darakta janar na sashen cibiyar bincike da jinsi na jami’ar Bayero dake jihar Kano farfesa Hassana Sani Darma tace mata sune jagaba a kullum wajen neman ayi musu adalci fiye da maza idan akayi la’akari da cin zarafin da ake musu.

Farfesa Hassana ta bayyana haka a taron jinsi da al’amuran kiwon lafiya da kungiyar Women’s Life Builders ta shirya tare da hadin guiwar ofishin mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin kiwon lafiya.

Wakilinmu a jihar Kano Ahmed Bachurawa ya rawito cewa Farfesa Darma ta bayyana cewa yayin da wasu suna kira a daidai ta yancin mata a lokaci guda, hakan yana illoli da dama a fuskar addinin musulunci kuma masuyin haka suna da wata manufa na daban.

Tace akwai damammaki dayawa day a kamata a baiwa mata amma ana hanasu samun damar ba tare da wata dalili kwakkwara ba sai dai akan cewa ita mace ce.

A nata bayani wadda ta shirya taron mai bada shawara na musamman ga gwamna kan harkokin kiwon lafiya Fauziyya Buba Idris tace manufar taron shine tattaunawa kan kiwon lafiya da ta shafi matsalar kwakwalwar mata.

A nata bangaren likitan masu matsalar kwakwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano Hajara Kabiru Shehu tace matsalar da ta shafi tabin hankali tana da illa a boye ga jama’a musamman ma mata da basu san da haka ba.

Tace mata da dama suna fama da damuwa wanda yake kai ga matsalar kwakwalwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply