Masu Daukar Ma’aikata A Najeriya Sunce A Shirye Suke Su Biya Kudin Da Aka Kayyade Na Albashi

nlc
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Masu daukar ma’aikata a Najeriya sun bayyana cewa a shirye suke su biya kudin da aka kayyade na biyan albashi idan aka maida shi doka.

Shugaban kungiyar daukar ma’aikata na kasa ne ya bayyana hakan yayin taron da akeyi karo na 107 na ma’aikatan na duniya a Geneva dake Switzerland.

Yayin da yake Magana da manema labarai shugaban kungiyar daukar ma’aikatan Olusegun Oshinowo ya bayyana cewa a shirye suke su biya ma’aikatan yadda aka kayyade din.

Haka nan shugaban ma’aikatan na kasar Najeriya Ayuba Wabba yace idan masu daukar ma’aikatan sun yadda suna iya farawa daga watan satumba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply