Masana Sun Gargadi Jama’a Kan Yadda Zasu kare kansu Daga Macizai Ta Hanyar Magudanan Ruwan Bayan Gida

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil ,Maiduguri
An samu martani bayan rasuwar jami’ar sojan saman Najeriya Lance Corporal Ogah Bercy da ke aiki da hukumar leken asiri ta DIA, wacce ta rasu sakamakon cizon maciji a bayan gida da ke ofishin na NAF Base Bill Clinton Drive Abuja.

Tambayoyi kan yadda macizai da sauran dabbobi masu rarrafe ke shiga bandaki da bayan gida da dama sun taso a shafukan sada zumunta.

Bincike ya nuna cewa ba kasafai ake samun maciji a bandaki ba.

Yawancin masu aikin famfo sun ga maciji a ƙarƙashin gidaje ko a cikin bandaki, duk da haka, macizai na iya shiga bayan gida ta hanyar budewa magudanar ruwa.
Magudanar ruwa na iya zama wurin buya ga beraye da sauran dabbobi masu kama dasu.
Haka nan Macizai na iya shiga magudanar ruwa don samun abincinsu na gaba.

Za su iya yin hanyarsu ta cikin magudanar ruwa kuma su ratsa ta.
Lokacin da ake magana game da shigar macizai cikin bayan gida, wasu suna tunanin ko kuma suna ɗauka cewa akwai ruwa a cikin kwalbatin ɗin bayan gida, amma bisa ga masu aikin famfo, an tsara kujerar bayan gida ta yadda ruwan zai a tsaya a cikin kwalbatin kawai ta yadda bututun zai iya tsayawa.

Yawancin dabbobi masu rarrafe suna da wahalar tsalle ko shiga cikin ɗakunan ruwa, koyaushe suna samun sauƙin shiga daga ɗakunan simintin da ke bayan gidan.

ta inda ake haɗa bututun najasa da kuma inda ya tsage, ƙarƙashin ƙofofi da ramuka.

Ga wasu matakan kariya da za ku ɗauka waɗanda za su taimaka wajen guje wa macizai a cikin kwanon bayan gida;
A tattaunawarsa da gidan rediyon Dandal Kura Sale Kadai wani ma’aikacin famfo ya yi gargadin cewa, hanya mafi kyau da za ta hana maciji shiga bandaki ita ce ka sa gidanka ya zama mai tsafta tun da farko.

Ya kara jaddada cewa a rufe tagogi da kofofin cikin ban daki ko kuma tabbatar da cewa fuskar ta cika ta yadda maciji ba zai iya shiga ba.

Ya ce hanyar kariya daga macizai na da nasaba da kawar da beraye a kusa ko a cikin gida.
MNT/COV/BBW

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply