Manoma sun nuna gamsuwar su game da kokarin jami’an sojoji na yaki da yan fashi da makami.

Kungiyar manoma ta Najeriya tace ta samu kwarin guiwa game da matakin da sojojin kasa suka dauka na cigaba da yakai yan bindiga a wasu jihohin arewacin kasar.

Shugaban kungiyar Mr. Faruk Mudi shi ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.

Kungiyar dukkan manoma ta Najeriya wato AFAN kungiya ce ta dukkan manoman kasa.

Yace manoma sune na farko da rashin tsaro ya fi shafa sakamakon kashe yawancin mambobin su da akayi a gonakin su.

Yace bazasu gajiya ba wajen komawa gonakin su saboda shugaba Buhari ya damu matuka a kan yaki da rashin tsaro a kasar nan kuma yana iya kokarin shi wajen magance matsalar.

Daga karshe yace suma manoma a yanzu suna maida hankali a al’amuran su na yau da kullum yayin da suke hada kai a jami’an yan sanda da sojoji kan duk wani abun da basu gane ba.