Manajan Daraktan Gidan Radiyon Dandal Kura International Alh Faruq Dalhatu Ya Baiyana Alhinin Sa Kan Rasuwar Janaral Manajansa Alhaji Ibrahim Elhusain Wanda Ya Rasu A Jihar Kano A Safiyar Yau 12 12 2020.

faruk-dalhata-chef-vom-radio-sender-da
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil, Maiduguri

Mahukuntan gidan Radiyon Dandal Kura na nuna alhinin rasuwar Janaral Manajanta Alhaji Ibrahim Elhusain wanda ya rasu a jihar Kano a safiyar yau 12 12 2020.

Manajan Daraktan Gidan Radiyon Dandal Kura Radio International da FM 98.9 Maiduguri Alh Faruq Dalhatu ya tabbatar da rasuwar marigayin inda yace ya rasu yana da shekaru 61.

Alhaji Faruq Dalhatu yace marigayi Elhusain kwararren dan jarida ne da ya bada gudunmawa da dama wajen ayyukan cigaban aikin jarida dama ayyukan yada zaman lafiya dama tabbatar da cigaban kasar Najeriya.

Haka nan yace marigayi Alhaji Ibrahim Elhusain mamba ne a kungiyoyi da dama ciki harda Nigerian Guild of Editors (NGE) da kuma World Editors Forum (WEF).

Alhaji Faruq Dalhatu ya kara da cewa za’a dinga tunawa da marigayin wajen jajircewarsa, kwarewarsa, kokarinsa da rike aikinsa yadda ya kamata.

Marigayin ya rasu ya bar matarsa, yayansa, yanuwansa mata da maza inda tuni aka binne shi a jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya kamar yadda addinin musulinci ya tanadar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply