makiyaya da manoma Jami’an soji sun kashe kwamandojin Boko Haram guda 2 a jihar Borno

chibok-school-troops-nigeria-330x242
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Jam’an sojin Najeriya karkashin operation Tura ta Kai Bango dake karkkashin Operation Lafiya Dole sun kashe wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram da hukumomi suke nema ruwa a jallo Abul-Bas da Ibn Habib.

Rundunar tace sun samu nasarar a kwantan bauna da sukayi wa yan kungiyar akan hanyarsu tsakanin Buria da Guja da suke bi don tsallakawa a titin banki zuwa Pulka a jihar Borno.

Rahoton na rundunar da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar ya fitar Brigadier General Mohammed Yerima yace jami’an naci gaba da bawa yan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP kashi.

Jami’an sun samu nasarar samun bindigar GPMG guda, AK47 guda 7 , belt mai harsashai 446 mai tsawon milimita 7.62, babur 1 da kuma wayar tafi da gidanka guda 1 mai kirar ITEL 2160.

Abul-Bas da Ibn Habib na cikin manyan yan kungiyar Boko Haram dake bangaren Shekau wanda ke aiki tsakanin dajin Sambisa da kewaye.

Kwamandojin 2 dai na cikin wadanda jami’an tsaron sirri suke nema ruwa a jallo tsawon lokaci.

Inda Abul-Bas shine kwamanda na 2 daga Abu Fatima sai Ibn Habib wanda kwamanda ne dake kula da yankin Njimia da Parisu a dajin Sambisa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply