Makarantar sashin bincike na yankin tabkin chadi tayi ta’aziya ga gwamnati da jama’ar jihar Borno bisa rasuwar mai martaba shehun Dikwa.

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Makarantar sashin bincike na yankin tabkin chadi tayi ta’aziya ga gwamnati da jama’ar jihar Borno bisa rasuwar mai martaba shehun Dikwa.

Amadadin hukumar gudanarwa na makarantar da daukacin ma’aitana su, mukaddashin babban daraktan makarantar Dr. Alhasan Sabo Bibinu yayi ta’aziyar gwamna Babagana Umara Zulum bisa rashin mai martaba Alh. Muhammad Ibn Shehu Masta na biyu Elkanami.

Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mika ga wakilin mu Nura Umar ta hannun shugaban yada labarai Muhammad Abba Sadiq.

Sanarwar ta kara dacewa babban daraktan makarantar ya bayyana wannan rashi da cewa babban rashi ne ba ma ga jama’ar Borno kadai ba har ma da kasa baki daya.

Daga karshe yayi addu’an Allah ya jikan sa da rahama ya kuma baiwa iayalan sa da jama’ar jihar Borno hakurin rashin sa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply