
Majalisar gudanarwa na jami’ar tarayya dake Gashua a jihar Yobe ta amince da nadin farfesa Maimuna Waziri a matsayin Vice-Chancellor na jami’ar.
Wannan ya fito ne bayan zaman da majalisar tayi karo na biyar da aka gudanar a karshen mako.
Zata maye gurbin farfaesa Andrew Haruna wanda lokacin aikin sa zai kare a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Bayanai ya nuna cewa mutane 48 ne suka nemi mukamin amma 25 kawai aka gana dasu, mutane 3 ne suka kai ga matsayi na karshe kafin majalisar ta daidaita da farfesa Maimuna.
A nashi bangaren Mal. Ibrahim Akuyam ya taya ta murna kuma yayi kira a gare ta da ta dauki kowa daidai.
