Majalisar Zartarwa Ta Jihar Borno Ta Ware Naira Biliyan 6 Domin Gudanar Da Ayyuka 18 A Jihar

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

From Hadiza Garba , Maiduguri
Majalisar zartarwa na jihar Borno ta ware naira biliyan 6 domin gudanar da ayyuka 18 da kuma ayyukan tsaro a jihar

Kwamishinan yada labarai da al’adu Baba Kura Abba Jato shi ya bayyana haka ga manema labarai a karshen taron majalisar karo na farko a wannan shekara wanda gwamna BG Zulum ya jagoranta a fadar gwamnatin jiha.

Kwamishinan ya kara dacewa majalisar ta ware naira miliyan dari 3 da 52 domin taimakawa jami’an sa kai na CJTF da maharba da kuma yan Vigilanti sannan an ware naira miliyan dari 6 da 58 domin gyaran titin Maiduguri zuwa Damboa da kuma tashan motar Bama da kasuwa.

Sauran ayyukan sun hada da kara aikin titin Benisheikh akan naira miliyan dari 2 da 31, da gini titin Ramat zuwa Wulari da kuma magudanan ruwa akan naira miliyan dari 2 da 37 da kuma ginin titin Ngomari dake tsohuwar filin jirgi.

Haka kuma majalisar ta ware kudade domin ginin sashen da ya shafi ciki da harkokin mata a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri akan naira biliyan 1 da digo 6, da ginin shaguna a Bulumkutu, da ginin ajujuwa 33 Buratai akan naira miliyan dari 2 da 52 da kuma takardu a makarantu da tsarin ciyarwa na makaranta da sauran su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply