Majalisar Wakilai Ta Kasa Ta Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro

NationalAssembly-OpinionNigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Majalisar wakilai ta kasa ta tantance sabbin hafsoshin tsaron kasa da aka nada
An gudanar da tantancewar ne cikin sirri bayan an yi bayani takaitacce.

Kafin a fara wasu daga cikin hafsoshin sun bayyana shirin su game da tsaro.

Shugaban hafsan tsaron kasa manjo janar Lucky Irabor yace niyyar sa shine rundunar tsaro ta zama tana gudanar da aiki cikin gaggawa da bin doka.

Haka kuma hafsan rundunar sojojin kasa manjo janar Ibrahim Attahiru yace zai tabbatar da kyakkyawan shugabanci ga rundunar musamman a wannan lokaci da kasa ke fama da matsala.

Tunda farko a nasa jawabin, shugaban kwamiti kan tsaro na majalisar Babajimi Benson yace majalisar zata tabbatar da gwamnati tayi aiki yadda ya dace.

A ranar laraban da ta gabata kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya karanta wasika daga shugaba Buhari inda ya nemi a tabbatar da nadin sabbin hafsoshin.

Daga baya kuma kakakin ya nada kwamiti da suka hada da shugaba, mataimakin shugaba da mambobin kwamiti da suka hada da sojoji wanda shugaban kwamiti kan tsrao na majalisar Mr Babajimi Benson zai jagoranta.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply