Majalisar Wakilai Sun Dakatar Da Gwamnatin Tarraya Shirinta Na Daukan Ma’aikata Dubu Dari Bakwai Da Saba’in Da Hudu.

reps
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Majalisar wakilai sunyi kira da a gaggauta dakatar da shirin gwamnatin tarraya na daukan ma’aikata aiki wanda ake ta jayyaya akai.

Majalisar dattawa da kuma ma’aikatar daukan aiyyuka suna ta cece- kuce a game da shirin daukan ma’aikata da gwamnatin tarraya take shirin yi.

A zama da sukayi jiya sun yi kira ga ma’aikatar kudi da tsare-tsare da kada ta bada kudi ga shirin wanda ana sa ran zai fara aiki a watan janairu cikin shekarar 2021.

A cewar Majalisar dattawan sun riga da sun nemi da abusu naira biliyan hamsin da biyu domin shirin tun cikin shekarar 2020 wanda ya kamata ace shirin ya kankama tun watan nuwamban da ya gabata.

Majalisar sun kuma nuna rashin jin dadinsu a game da soke shugaban hukumar ma’aikatan Dr Nasiru Argungu da akayi sunce yana aiki yanda ya dace.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply