Majalisar Tsaron Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta A Gaza

Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da tsagaita wuta wanda Masar ta shiga tsakani.

A rahotannin da DANDAL Kura Radio International ta hada a Maiduguri, tsagaita bude wutar ga Isra’ila da Falasdinu zai fara aiki ne da karfe 2 na dare a ranar Juma’a.

Sojojin Tsaron Isra’ila sun amince da tsagaita wuta bayan hare-hare ta sama da kwana goma sha daya da suka lalata sama da gine-gine 450 a Gaza.

Harin saman da aka kai a Gaza ya bar kayayyakin more rayuwa sun ruguje tare da jikkata mutane wanda ya nuna cewa kimanin mutane 233 suka mutu.

Daga cikin wadanda suka mutu, 60 daga cikinsu yara ne tare da dubbai da suka samu raunuka yayin da suke karbar magani a asibitoci.

Isra’ila ta ce tsagaita wutar, wacce Masar ta gabatar za ta kasance ne ba tare da wani sharadi ba.

Haka kuma, mayakan Hamas sun tabbatar da tsagaita wutar, suna masu cewa za su yi aiki da shi.

A halin da ake ciki, Tsaron Isra’ila ya sanar da shirin bama bamai kan wasu gine-ginen da aka yi niyya kafin tsagaita wuta a karfe 2 na dare a yankin na Gaza, yayin da suka shawarci wadanda ke zaune a ginin da abin ya shafa da su fice.