Majalisar Dinkin Duniya Sun Dakatar Da Ayyukan Jin Kai A Dikwa Da Damasak A Jihar Borno

Majalisar dinkin duniya Sun Dakatar Da ayyukan jin kai na wani dan lokaci Dikwa da Damasak a jihar Borno bayan hare-haren boko haram a wadannan yankuna.

Edward Kallon, mazaunin majalisar dinkin duniya kuma mai kula da ayyukan jin kai a najeriya, ya bayyana hakan ta hanyar wata sanarwa ranar asabar.

Yace, an dakatar da ayyukan jin kai a yankunan guda biyu domin tabbatar da tsaro sannan sun dauke ma’aikatan jin kai na agaji agurin domin kaisu wurare daban-daban don cigaba da ayyukan na jin kai.