Majalisar Dattijai Taki Amincewa Da Shugaba Buhari kan Cire shugaban Hukumar Samar Da Ayyukan Yi Ta Kasa

senatesmall
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Majalisar dattijai a ranar Alhamis ta nuna rashin amincewar ta ga Shugaba Muhammadu Buhari kan korar Darekta Janar na Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu.

Wannan cigaban ya zo ne a ranar Alhamis yayin zaman majalisar dattijai.

An gano cewa korar Argungu ya biyo bayan rikicinsa da karamin Ministan kwadago Festus Keyamo akan daukar mutane 774,000 aikin gwamnati.

Da yake duba a kan lamarin, Sanata Ibrahim Hadejia ya nuna rashin gamsuwa da cire shugaban shugaban Hukumar samar da ayyukan yi da Shugaba Buhari ya yi.

Majalisar Dattawa a cikin kudurin ta bukaci da a binciki alakar dake tsakanin Keyamo da shugaban samar da ayukanyi da aka sallama inda yace cireshin zai iya shafar daukar ‘yan Najeriya 774,000 aikin gwamnati.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply