
By Hassan Umar Shallpella, Yola
Mabiya addinin kirista a jihar Adamawa sunyi bikin kirismeti tare da bin dokar covid 19 na sanya takunkumin fuska, bada taraza da wanke hannu a wuraren ibadar su.
Mabiya addinin sunyi shige cikin kayakin su domin murnar bikin kirismeti a wuraren ibadu domin yin addu’o’I.
Haka kuma an samu kasancewar jami’an tsaro domin kare masu ibada a wuraren ibadar su.
A nashi jawabin sa Pastor Eli Barnabas yayi kira ga kiristoci da zu zama masu son zaman lafiya, gaskiya da kuma rikon amana tare da kawar da cin hanci a dukkan yanayi.

